Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labaran kasar Labanon sun rawaito a yau Juma'a cewa wani dan kasar Lebanon ya yi shahada tare da jikkata wasu uku a wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a kudancin kasar Lebanon.
Harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan wata mota a gaban asibitin gwamnati na "Tibneen" da ke kudancin kasar Lebanon.
Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mutum daya ya yi shahada yayin da wasu uku suka jikkata a harin.
Your Comment